Home Labaru Ilimi Hukunci: Wata Kotu A Abuja Ta Bukaci Saraki Da Dogara Su Bayyan...

Hukunci: Wata Kotu A Abuja Ta Bukaci Saraki Da Dogara Su Bayyan A Gabanta

398
0

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta ba shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kuma shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara su bayyana a gaban ta.

Alkali kotun mai shari’ar Okon Abang,  ya nemi sanatoci 18 da kuma ‘yan majalisun wakilai 36, da ministan shari’a na Najeriya, da mataimakan shugabannin majalisar dattawa Ike Ekweremadu da Yusuf Lasun su shirya zuwa gaban kotu.

Mai shari’ar Okon Abang, ya ce kotu na bukatar wadannan mutane su kare kan su game da karar su da ake yi akan sauya sheka daga wata jam’iyya zuwa wata a kwanakin baya.Alkalin ya ce ba wani sassauci, dole ne wadanda ake karar su, su  je kotu nan da ranar 18 ga watan Afrilu domin kare kansu.

Leave a Reply