Hukumar yaki da cin hanchi da Rashawa ta jihar Kano, ta ce
ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje
domin jin bayanai a kan wani faifan bidiyon da aka taba saki,
inda ake zargin shi da karbar daloli ya na cusawa cikin aljihun
sa.
Idan dai ba a manta ba, a watan oktoba na shekara ta 2018 ne Jaridar Daily Nigerian ta wallafa wani bidiyo da ake zargin Ganduje ne a ciki ana mika ma shi kudi ya na karba.
Biyo bayan alkawarin da ya yi na bin doka da oda game da binciken da ake yi a kan bidiyoyin da ake zargin Ganduje ya na karbar daloli, shugaban hukumar Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce hukumar ta aike wa tsohon gwamnan sammaci domin ya bayyana a gaban ta.
Rimin Gado ya fara sanar da batun gayyatar Ganduje ne yayin wata tattaunawa da shi a wani shiri na gidan talabijin na Channels, inda ya ce hukumar ta na sa ran Ganduje ya bayyana a gaban ta mako mai zuwa domin samun damar gyara sunan sa a kan binciken da ake yi.