Home Home Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Yi Wa Maniyyata 3,918 Rijista A Cikin...

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Yi Wa Maniyyata 3,918 Rijista A Cikin Kujeru 5,001 A Sakoto

143
0

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Sokoto, ta ce ta yi wa maniyyata aikin hajjin bana dubu 3 da 918 rajista domin tafiya aikin hajji kasar Saudiyya a shekara ta 2024, daga cikin kujeru dubu 5 da 1 da aka ware wa jihar.

Shugaban hukumar Alhaji Aliyu Musa-Gusau ya bayyana haka, bayan wata ganawa da jami’an mataimakan aikin hajji na kananan hukumomi 23 a Sokoto.

Musa-Gusau, wanda ya samu wakilcin Daraktan gudanarwa na hukumar Alhaji Ladan Ibrahim, ya ce hukumar za ta rufe karbar kudaden yin rijistar aikin Hajjin shekara ta 2024 a ranar 12 ga watan Fabrairu.

Ya ce rufe rajistar ya dogara ne da umarnin hukumar alhazai ta kasa cewa a kammala dukkan biyan kudade da kuma sayen kujera zuwa ranar Litinin 12 ga watan Fabrairu.

Leave a Reply