Hukumar kiyaye hadurra ta kasa ta gargadi jami’an ta su daina bin masu laifi a guje ko da kuwa sun aikata laifi.
Jami’i mai kula da sashen wayar da kan jama’a na hukumar Bisi Kazeem ya bada wannan sanarwa, yayin da ya zanta da manema labarai a Lagos.
Kazeem ya bayyana haka ne, a daidai lokacin da ya ke jawabi akan hadarin da ya auku ranar Juma’a a garin Ibadan sakamakon bin masu laifin da jami’an hukumar su kayi.
Ya ce hakika Shugaban hukumar ya nuna bacin ran sa bisa faruwar wannan hatsari, duba da cewa dokar aikin su ta hana jami’i ya rika bin mai laifi a guje duk kuwa girman laifin sa, saboda a tsanake ta hanyar lambar abin hawa za a iya kama mai laifi a cikin ruwan sanyi.
Jami’in ya ce, a matsayin su na hukuma mai aiki a kan dokoki za su bi kadin lamarin, kuma ya zama dole a yi bincike, sannan idan aka samu wani jami’in su da laifi za a yi ma shi hukuncin da ya dace da shi.
You must log in to post a comment.