Home Labaru Labarun Ketare Hukumar Ƙwallon Ingila Na Tuhumar Osmajic Da Cizo Ana Tsaka Da Wasa

Hukumar Ƙwallon Ingila Na Tuhumar Osmajic Da Cizo Ana Tsaka Da Wasa

24
0
GettyImages 2172946781.jpg
GettyImages 2172946781.jpg

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila (FA) ta tuhumi ɗanwasan gaba na Preston North End Milutin Osmajic da haddasa tashin hankali bayan an zarge shi da cizon ɗan wasan baya na Blackburn Rovers, Owen Beck.

Beck da yaje wasan aro daga Liverpool, an kore shi ne saura minti kaɗan a tashi daga wasan ranar Lahadi na hamayya saboda dukan Duane Holmes na Prestone.

Daga nan ne kuma aka fara hatsaniya, inda Beck mai shekara 22 ya yi wa lafari ƙorafin cewa Osmajic ya cije shi.

Bidiyon da aka maimaita daga baya ya nuna Osmajic yana cizon Beck a baya.

FA ta ce an ba Osmajic nan da ranar Litinin, 30 ga watan Satumba don kare kan sa.

Leave a Reply