Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta kasa NSCDC sun lalata
wata haramtacciyar matatar danyen mai a dajin Odagwa da ke
Karamar Hukumar Etche a Jihar Ribas.
Kakakin hukumar a Jihar Ribas, Oufemi Ayodele, ya ce matakin na daga cikin yaki da satar danyen mai da a ke yi a kasar nan.
Hukumar ta gudanar da wannan aiki ne ba sani ba sabo, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa wajen yaki da satar danyen mai Nijeriya ba, wannan babbar nasara ce.