Home Labarai Hayaƙin Janareta Ya Kashe Mutum Bakwai A Bayelsa

Hayaƙin Janareta Ya Kashe Mutum Bakwai A Bayelsa

263
0
360 F 356316372 tGZ4gG7sHHh2vBT2GIgIpd9LO2klumgd
360 F 356316372 tGZ4gG7sHHh2vBT2GIgIpd9LO2klumgd

Mutum bakwai sun mutu sakamakon hayaƙin injin janareto da ya mamaye ɗakin da suke kwace a Yenagoa,

an samu gawarwakin mutanen galibin su ɗaliban Jami’ar Niger Delta a cikin dakin kiɗe-kiɗe watau ‘studio’ ranar Talata da safe, bayan sun shaƙi hayaƙin injin.

Rahoton ya ce sutudiyan na ɗaya daga cikin mutanen da suka mutun ne.

An ce a ranar Litinin da daddare ne marigayan suka fara aiki a sutudiyan, sai barci ya ɗauek su sakamakon gajiyar da suka yi, ba tare da sun kashe injin ba.

Sai dai ko da gari ya waye ranar Talata, sai aka samu gawar mutum shida daga cikin su,

yayin da ɗayan ke cikin mawuyacin hali inda nan take aka garzaya da shi asibiti, kafin shi ma ya mutu a asibitin.

Hayaƙin janareta dai na ɗauke da wani sinadari da ke toshe hanyoyin shaƙar iska, lamarin da ke barazana ga rayukan mutane.

Leave a Reply