Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Hatsari: Wani Jirgin Sama A Dubai Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutum Hudu

Wasu mutum hudu ne suka mutu sanadin wani hatsarin jirgin sama da ya fado kimanin kilomita uku, yamma da babbar tashar jigin saman Dubai.

Hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa sun ce uku daga cikin mamatan ‘yan Birtaniya ne, daya kuma dan Afirka ta Kudu.

Dukkan su na cikin jirgin samam ne samfurin DA42, mai iya daukar mutum hudu, mallakin kamfanin Flight Calibration Services da ke tashar jirgin sama na Shoreham a yankin West Sussex na Ingila.

Rahotanni daga kafafen yada labarai na Dubai na cewa jirgin ya fado ne, inda direban jirgin da mataimakin sa da kuma fasinjoji biyu dake cikin jirgin suka gamu da ajalin su. An rufe tasahr jirgin sama na Dubai har tsawon minti 45 bayan hatsarin, inda aka karkatar da akalar wasu daga jiragen sama da ke neman izinin sauka da fasinjojin su.

Exit mobile version