Home Labaru Hasashe: Akwai Fargaba Kan Tattalin Arzikin Duniya A Bana- IMF

Hasashe: Akwai Fargaba Kan Tattalin Arzikin Duniya A Bana- IMF

236
0

Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF ya bayyana fargaba kan hasashen koma baya da ya samu na tattalin arzikin duniya a watanni ukun wannan shekara.

Rahoton hasashen Asusun na IMF ya bayyana manyan batutuwan da suka haifar da koma bayan da aka samu da suka hada da matsalolin cinikayya da batun ficewar Birtaniya daga kungiyar Turai dama sauran muhimman dalilai.

A cewar asusun na IMF matukar ana fatan warwarewar matsalolin da suka haifarwa tattalin arzkin koma baya, dole ne a kawo karshen takaddamar cinikayya tsakanin Amurka da China.

Babban Jami’in da ke kula da tattalin arziki na IMF Gita Gopinath, ya ce tafiyar hawainiyar da tattalin arzikin duniya ya yi a watanni ukun farkon shekarar nan ya kai kashi 70 a cikin 100 matakin da ke nuna babban koma baya.

Rahoton asusun ya kuma nuna cewa kasashen da ke amfani da kudin Euro, anan abin ya fi kamari, musamman kasar Jamus inda aka sami kashi 50 cikin dari na hasashen habakar tattalin arzikin da aka yi cikin shekarar nan, yayinda a kasar Italiya kuma tattalin arzikin a tsaya cik.

Ka zalika rahoton na IMF na nuna cewa takaddama kan shirin ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai zai sanya kasar zamowa ‘yar gaba gaba a jerin kasashen Turai da za su samu koma bayan tattalin arziki a bana.

Leave a Reply