Home Labaru Harin ‘Yan Bindiga: Gwamnan Zamfara Zai Gana Da Kwararru A Fannin Tsaro...

Harin ‘Yan Bindiga: Gwamnan Zamfara Zai Gana Da Kwararru A Fannin Tsaro A Kasar Dubai

450
0
Bello Matawalle
Bello Matawalle

Yayin da ‘yan bindiga ke ci-gaba kai hare-hare a kauyukan jihar Zamfara, Gwamna Bello Matawalle zai gana da kwararru a fannin tsaro a kasar Dubai domin tattauna hanyoyin magance lamarin.

A cikin wata sanarwa da Babban Daraktan yada labarai na gidan gwamnatin jihar Zamfara Yusuf Idris ya fitar, ya ce gwamnan wanda ya tafi kasar Saudiyya a ranar Lahadin da ta gabata, zai tsaya a Dubai domin haduwa da kwararru a fannin tsaro don neman shawarwarin su.

Ya ce Gwannan zai hadu da kwararru a fannin tsaro a Dubai inda za’a tattauna hanyoyin kawo karshen lamarin hare-haren da yan bindiga ke kai wa a jihar.

Yusuf Idris ya kara da cewa, ana zatton gwamnan zai hadu da jami’an gwamnatin Saudiyya domin tattaunawa a kan yadda za a kubutar da Alaramma Ibrahim haifaffen jihar Zamfara da ke tsare kusan shekaru biyu bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.

A karshe ya ce gwamnan zai kuma hadu da ma’aikatan bankin ci-gaban Afrika da wassu masu hannun jari da ke da niyyar zuba hannun jari a tattalin arzikin jihar Zamfara.