Home Labaru Harin ‘Yan Bindiga: Al’ummomi Na Ci-Gaba Da Kaurace Wa Muhallansu A Jihar...

Harin ‘Yan Bindiga: Al’ummomi Na Ci-Gaba Da Kaurace Wa Muhallansu A Jihar Katsina

927
0

Rahotanni daga jihar Katsina na cewa, yanzu haka al’ummomin kauyukan kananan hukumomin Batsari da Safana na ci-gaba da kaurace wa muhallan su sakamakon ta’azzarar hare-haren ‘yan bindiga da gwamnatin jihar ta kasa daukar mataki a kai.

Da yammacin ranar Talatar da ta gabata ne, ‘yan bindiga dauke da manyan makamai su ka afka wa kauyen Wagini da ke karamar hukumar Batsari, inda su ka yi ta’adi tare da yin awon gaba da dukiyoyin jama’a.

‘Yan bindigar, sun kuma kai hari a kauyen Gora II da ke karamar hukumar Safana, inda su ka kashe mutane uku, sannan su ka balle duk shagunan kasuwanci da ke garin tare da kwashe dukiya mai tarin yawa, baya ga dabbobin da su ka yi awon gaba da su da ba a san adadin su ba.

Gwamnatin jihar Katsina dai ta kasa tabuka abin a zo a gani ta fuskar daukar matakin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar kananan hukumomin biyu.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun ci karen su ba babbaka yayin da su ka shiga garin Gora II, inda su ka kwashe tsawon sa’o’i su na gallaza wa mutane ba tare da daukin jami’an tsaro ba.

Leave a Reply