Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatin tarayya ba za ta kyale duk wanda aka samu da hannu a halaka rayuka da dukiyoyin jama’a a jihohin Zamfara da Katsina da kuma Kaduna ba.
Buhari wanda yayi Allah wadai da aikin ‘yan fashi a jihohin uku, ya ba shugabannin tsaro umurnin yin duk abin da ya kamata cikin kankanen lokaci su dakile ayyukan ta’addanci a yankunan jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne ta bakin Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, wanda ya samu rakiyar shugabannin tsaro na jihar zuwa ziyara kauyukan ‘Yar Santa da Tsamiyar Jino a karamar hukumar Kankara, domin yi wa mutanen yankin jajen hare-haren ta’addanci da aka kai garuruwan.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara a kafofin yada labarai Abdu Labaran Malumfashi ya fitar, Masari ya ce lamarin ba abin yarda ba ne, inda ya bada tabbacin shirin da gwamnati ke yi na magance matsalar.