An yi jana’izar akalla mutane 14 da su ka mutu sakamakon wani mummunan hari da ‘yan bindiga su ka kai kauyen ‘Yancala Gobirawa da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.
Dan majalisar dokoki ta jihar Katsina mai wakiltar yankin Abdul-Jalal Haruna Runka ya shaida wa manema labarai cewa, maharan sun kai farmakin ne a kauyukan ‘Yancala Gobirawa da kuma Sha-ka-Fito.
Ya ce ‘yan bindigar sun kashe mutane 11 a Gobirawa, yayin da aka kashe wasu mutane uku a kauyen Sha-ka-Fito, baya ga wadanda su ka jikkata da dama.
Wata majiya ta ce yawancin mutanen da su ka mutu an kashe su ne a cikin gonaki saboda ‘yan bindigar sun fara firgita garin ne, lamarin da ya sa kowa ya yi ta kan sa.