Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Harin Rijana: Babban Hafsan Sojin Nijeriya Ya Kai Ziyara Inda Aka Kai Wa Jirgin Ƙasa Hari

Babban hafsan sojin ƙasa na Nijeriya laftanar Janar Faruk Yahaya, ya kai ziyara inda aka kai wa jirgin ƙasa hari a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Babban hafsan sojin ƙasa na Nijeriya laftanar Janar Faruk Yahaya, ya kai ziyara inda aka kai wa jirgin ƙasa hari a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Rundunar sojin Nijeriya ta wallafa hotunan sa a shafin Facebook tare da tawagar sa a wurin da lamarin ya faru, inda ta ce ya je ne domin duba yanayin wurin da girman harin.

Janar Faruk Yahaya, ya kuma umarci sojoji su tsawaita bincike domin kuɓutar da mutanen da aka sace.

Bayanai sun nuna cewa, kimanin mutane 1000 ne a cikin jirgin da aka kai wa harin, inda aka kashe wasu tare da sace wasu da dama.

Exit mobile version