Home Labaru Harin Rabah: Wasu Mazauna Sakkwato Sun Koka

Harin Rabah: Wasu Mazauna Sakkwato Sun Koka

432
0

Harin da aka kai ranar Asabar data gabata wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutum 25 a wasu kauyuka na karamar hukumar Rabah dake jihar Sokoto ya bar baya da kura.

Kauyen Rakwabni ne aka fi yima barna inda aka kashe mutum sha bakwai ciki hadda yarin ya yar shekara 6.

Garin na kilomita 7 ne daga garin Gandi dake a Rabah, inda a halin yanzu mazauna garin duk sun yi kaura.

Bayan sun gama hargitsa garin, yan ta’addan sunyi awon gaba da shanun al’ummar garin wanda suke amfani dasu wajen aikin gona.

Wasu Kauyukan da abin ya shafa sun hada da Bedi, da Kalfu-Tsege,  da Kwalfa Agaji, da Kaiwa gari.

Babban limamin garin Rakwabni kuma shugan ‘yan banga na kauyen, Malam Dahiru, ya ce kafin akai harin, Rakwabni ne kadai kauyen da ya rage ba akai ma hari ba.

Malam Dahiru ya kara da cewa sau dayawa suna fuskantar ‘yan ta’adda su kwace shanun da suka sato daga mutane sa’annan su mayar ma mutane da shanun su. Yace Sabida haka wannan harin da suka kawo ramuwar gayya ce saboda abinda ake masu, sai ya kara da cewa ‘yan ta’addan sun san basu iya masu, shi ya sa suka yi masu kwantan bauna.