Rundunar sojin Nijeriya ta kori wasu jami’an ta 8 daga aiki bayan an zarge su da tserewa daga sansanin su, bayan mummunan harin da mayakan kungiyar Boko Haram su ka kai wa sojoji a kauyen Metele da ke karamar hukumar Guzamala a jihar Borno.
Sojoji da dama da su ka hada Laftanal Kanal Ibrahim Sakaba, sun rasa ran su sakamakon harin da aka kai sansanin sojin a watan Nuwamba na shekara ta 2018. J
Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, an gano sojojin sun gudu ne bayan an gudanar da kidaya a sansanin su, sai dai wasu daga cikin su sun bayyana bayan wata guda da kai harin.
A ranar 19 ga watan Afrilu, mukaddashin kwamandan rundunar soji ta 157 Manjo UI Lezuya, ya bada umarnin gudanar da bincike domin gano dalilin bacewar sojoji da kuma bayyanar su daga baya.
Majiyar ta ce, ta ce binciken da aka gudanar ya hada da gano lokacin da sojojin su ka bar sansanin, da dalilin su na yin hakan da kuma dalilin dawowar su bayan shafe kwanaki ba su nan.