Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta cafke daya daga cikin fursunonin kurkukun Kuje da suka tsere a lokacin da yake shirin tafiya Jihar Kano.
’Yan sandan sunce, an kama fursunan mai suna Ali Shu’aibu ne, da misalin karfe 7.30 na Yammacin ranar 17 ga wata Yulin da muke ciki.
Wata sanarwar da jami’in hulda da Jama’a na jihar, DSP Muhammed Jalige ya fitar, ya ce fursunan mai shekaru 60 Dan Asalin Jihar Kano.
DSP Jalige ya ce fursunan yana daya daga cikin wadanda suka tsere daga gidan gyara hali na Kuje da ke Abuja.
Tuni dai Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Yekini A. Ayoku, ya ba da umarnin a dauki matakan da suka dace gabanin mayar da fursunan inda ya fito.
Idan za’a iya tunawa a Ranar 5 ga watan Yuli ne wasu ‘yan Bindiga suka kai hari gidan gyara halin na Kuje inda suka kubutar da daruruwan fursunoni ciki har da ’yan ta’addan Boko Haram da dama.
Tun bayan kai harin ne Hukumar Kula da Gidajen Gyara Hali ta Najeriya, ta fitar da sunaye da fuskokin ’yan ta’adda 69 daga cikin fursunonin da take nema ruwa a jallo.
You must log in to post a comment.