Home Labaru Harin Kogi: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Biyu A Wani Coci

Harin Kogi: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Biyu A Wani Coci

17
0

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari wani cocin ECWA a yankin Okedayo a jihar Kogi inda suka kashe mutum daya da sace wasu mutum biyu.

Rahotannin da ke fitowa daga yankin sun ce maharan sun auka wa cocin ne a lokacin da ake ibada ranar Lahadi.

Rahotannin sun ce ‘yan bindigar sun kashe wani Mista Gbenga Reuben kuma sun yi awon gaba da wasu maza biyu manya.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Kogi ta ce mutanen da suka jikkata a harin na samun kulawa a asibiti.

Ta kuma tabbatar wa mutanen garin cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaro a yankin.