Home Home Harin Kauyuka 15: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Maza Da Sace Mata Sama...

Harin Kauyuka 15: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Maza Da Sace Mata Sama Da 20 A Gusau

146
0

Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa mahara sun sace sama da mata 20, bayan jerin hare-hare da suka kai a kauyuka 15 da ke yankin babban birnin jihar, wato Gusau.

Wasu mazauna kauyukan Geba, da Tsakuwa, da Gidan Kada, da Gidan Kaura da ma karin wasu kauyukan da ke karkashin karamar hukumar ta Gusau, sun shaida wa BBC cewa maharan sun afka musu ne ranar Asabar, inda suka kashe mazaje tare da kona dukiyoyi, suka kuma kwashi mata da ‘yan mata suka wuce da su.

Mazauna yankunan sun ce a Kura an dauke macce 10, a Bayauri sun dauki tara, sun kuma shiga wani kauye Gana sun dauki bakwai, daga nan kuma suka ketara Duma suka dauki wasu bakwai kafin wayewar garin Lahadi.

Bugu-Da-Kari wasu da suka tsallake rijiya da baya a kauyen Kura sun ce an kashe musu mutun bakwai.

A yanzu rahotanni sun ce kauyuka da dama sun fara zama kufayi, yayin da mazauna ke gudun hijira zuwa Gusau.

Leave a Reply