Home Labaru Harin Daura: ‘Yan Bindigar Da Su Ka Sace Magajin Garin Daura Sun...

Harin Daura: ‘Yan Bindigar Da Su Ka Sace Magajin Garin Daura Sun Tuntubi Iyalan Sa

477
0

Masu garkuwa da mutanen da su ka sace Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar Uba, sun tuntubi iyalan sa bayan wasu sa’o’i  da sace shi kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

‘Yan bindigar dai sun sace babban basaraken ne a gaban gidan sa da ke garin Daura jim kadan bayan kammala salar Magariba a ranar Larabar da ta gabata.

‘Yan bindigar dai sun kashe wayoyin basaraken bayan sun yi awon gaba da shi, amma daga bisani sun ba shi damar yin magana da iyalan sa a takaice kamar yadda wani na kusa da da iyalan basaraken ya shaida wa manema labarai.

Magajin Garin ya tabbatar wa iyalan sa cewa ya na hannun masu garkuwa da mutanene.Magajin garin dai ya taba rike mukamin shugaban hukumar yaki da fasa-kwauri ta Nijeriya kuma kani ne ga Sarkin Daura.]�,y ��

Leave a Reply