Home Labaru Harin Birnin Gwari: ‘Yan Bindiga Sun Bude Wa Taron Biki Wuta A...

Harin Birnin Gwari: ‘Yan Bindiga Sun Bude Wa Taron Biki Wuta A Kauyen Kakangi

803
0

Yanzu haka ana cikin zullumi a kauyen Kakangi da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, sakamakon wani hari da ‘yan bindiga su ka kai kauyen a wani waje da ake gudanar da shagulgulan biki.

‘Yan bindigar dai sun dira kauyen ne da misalin karfe 5 na yamma a kan babura, inda nan take su ka bude wuta su na harbin kan-mai-uwa-da-wabi a wani ofishin ‘yan sanda, kafin da ga bisani su ka fara bi gida-gida su na kashe mutanen da su ka taras a ciki.

Rahotanni sun ce mutane da dama sun mutu yayin da aka tabbatar da jikkatar mutane shida, cikin su kuwa har da kananan yara, wadanda aka garyzaya da su babban asibitin Birnin Gwari domin yi masu magani.

A cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, shugaban kungiyar sa-kai a kan zaman lafiya da shugabanci nagari na karamar hukumar Birnin Gwari Ibrahim Abubakar Nagwari ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ‘yan ta’addan sun cinna wa gidaje da dama wuta a kauyen.

Leave a Reply