Ma’aikatar tsaron Afganistan ta ce mahara sun dasa bam a
karkashin kujerar wata mota a tsakiyar birnin Ghazni da ke
tsakanin birnin Kabul da Khandahar.
Hukumomin gwamnatin sun tabbatar da mutuwar fararen hula
akalla 15, wasu da dama sun jikkata a sabon harin bam da
mayaka suka tayar yayin da al’ummar musulmi ke taron karatun
Al-Kur’ani.
Sai dai ya zuwa yanzun babu kungiyar da ta dau alhakin harin
amma dama dakarun gwamnati da mayakan Tliban sun sha
dauki ba dadi a lardin Ghazni.
Kuma sabon harin yazo ne bayan wani kazamin harin kunar
bakin wake da ya kashe jami’an tsaro 30.
Duk dai wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnati ke
shirin sasantawa da mayakan Taliban.
You must log in to post a comment.