Ƴan Boko Haram sun kai hari a wani sansanin sojoji da ke Borno, inda suka kashe wasu sojoji, sannan ake tunanin sun yi awon gaba da wasu makamai.
Wata majiya ce ta tabbatar da haka inda ta ce mayaƙan Boko Haram na ɓangaren IS ne suka kai farmakin a sansanin soji da ke garin Kareto a ranar Asabar.
Majiyar ta ce an kashe kusan sojoji 20, amma shedkwatar tsaro ta Najeriya ta ce sojoji biyar aka kashe mata a harin.
Sai dai majiyar ta ƙara da cewa an gwabza yaƙi sosai tsakanin ƴan Boko Haram da sojojin, sannan wani ɗan ƙunar bakin wake ya tayar da motar da yake ciki, wanda a ƙarshe ƴan Boko Haram suka ƙona motocin sojoji 14.
A nata ɓangaren, gwamnatin jihar Borno ta yi wa sojojin Najeriya jaje bisa rasa jami’an ta a garin na Kareto.














































