Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Hare-Haren Zamfara: ‘Yan Ta’adda Sun Kashe Mutane 3000 – Yari

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce akalla mutane dubu 3 da dari 5 da 26 ne suka mutu cikin shekaru 5 da fara rikicin jihar da ya shafi kauyuka kimanin 500.

Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar, ya bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Gusau babban birnin jihar, inda ya ce yanzu haka akwai majinyata fiye da dubu 8 da 219 wadanda ya ce dukkanin su na cikin mawuyacin hali.

Taron wanda ya samu halartar mukaddashin sufeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Gwamnan ya ce akwai kuma fadin gona akalla kadada dubu 13 da yanzu haka ba a iya noma wa saboda ayyukan ‘yan ta’addan.

Gwamnan na Zamfara ya cigaba da cewa ce babu shakka hare-haren ‘yan ta’addan ya haddasa koma baya ga tattalin arzikin jihar wanda ya tilasta kulle kasuwanni da shagunan cinikayya, baya ga tilastawa daruruwan jama’a kauracewa muhallan su.

Abdul’aziz Yari ya ce gwamnatin sa ta tattara bayanan sirri kan hare-haren ‘yan ta’addan mai dauke da shafuka dubu 7, wanda ya ce akwai alaka tsakanin hare-haren ‘yan ta’addan da Kungiyar Boko Haram. A cewar sa Gwamnati ta gano wasu sansanin ‘yan bindigar har guda 8 a cikin dazukan kuma ta na fatan Gwamnatin Najeriyar ta dauki matakin kakkabe su cikin gaggawa.

Exit mobile version