Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Hare Hare: Miyetti Allah Ta Kare Kanta

Miyetti Allah

Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah reshen Kudu maso gabashin Najeriya ta yi ikirarin cewa mafi yawan kashe-kashen da ake yi a yankin na Kudu maso gabas ba, Fulani bane ke yinsa, wasu ‘yan bindiga ne da basu da wata alaka da Fulani.

Shugaban kungiyar reshen Kudu maso gabas, Siddiki Gidado, ya ce duk da yake za a iya samun bata gari cikin kungiyarsu, ya kara da cewa akasarin kashe-kashen ba mutanensu ba ne ke aikatawa.

Shugaban ya ce, mafi yawancin kashe-kashen makiyaya ne daga kabilun Igbo da Tiv, Bare-bari da Shuwa Arab ke aikata ta’asar amma ba Fulani makiyaya ba

Gidado ya ce a cikin ko wace kabila akwai Bara-Gurbi, idan aka samu bangare guda ya aikata laifi sai a tuhumi dukkanin al’ummar wannan kabilar, saboda haka ana yawan daurawa Fulani alhakin laifin da basu aikata ba.

Exit mobile version