Home Home Harbe Lauya:  Ƴan Sanda Sun Fadi Sunan Jami’in Su Da Ake Zargi

Harbe Lauya:  Ƴan Sanda Sun Fadi Sunan Jami’in Su Da Ake Zargi

37
0
‘Ƴan sanda a jihar Lagos sun sanar da sunan jami’in su da ake zargi da harbe wata lauya har lahira a birnin Legas a ranar Kirstimati.

‘Ƴan sanda a jihar Lagos sun sanar da sunan jami’in su da ake zargi da harbe wata lauya har lahira a birnin Legas a ranar Kirstimati.

Mrs Omobolanle Raheem, ta gamu da ajalinta ne a unguwar Ajah yayin da take kan hanyarta ta komawa gida daga addu’o’in zagayowar ranar ta Kirtimeti.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin ‘yan sanda a jihar SP Benjamin Hundeyin ya ce wanda ya harbe matar shi ne Drambi Vandi wanda kuma tuni aka kama shi kuma aka garkame.

SP Hundeyin, ya ce an kuma mika jami‘in mai mukamin mataimakin sufurtanda wato ASP ga sashen binciken miyagu laifuka na rundunar, kana ya yi alkawalin cewa ba za a bata lokaci ba wajen binciken kisan matar.

A ranar Lahadi ne aka harbe Mrs Bolanle Raheem, a unguwar Ajah lokacin da take kan hanyarta ta dawowa daga majami’a a kan idon mijinta da ‘ya’yanta da kuma kanwarta.