Wata ɗaliba musulma a wata makaranta a birnin Landan ta yi rashin nasara a wata babbar kotu kan ƙarar da aka shigar ta haramta yin sallah.
Yarinyar dai ta shigar da ƙarar makarantar Michaela da ke Brent a gaban kuliya saboda hana sallah wani mataki da ake ganin wariya ne.
A baya, makarantar wadda ba ta addini ba ce ta shaida wa kotun cewa ba da damar a yi sallah zai gurgunta tsarin tafiya da kowa tsakanin ɗalibai.
Mamallakin makarantar da babban malama, Katharine Birbalsingh ta ce hukuncin nasara ce ga dukkan makarantu.
A hukuncin mai shafi 83 da ya kori ƙarar ɗalibar, alƙali Linden ya ce shiga makarantar, kamar yarda da tsarin ne cewa za ta fuskanci wasu dokoki game da yin ibadun ta.
Kimanin rabin ɗaliban makarantar kusan 700 musulmi ne, kamar yadda aka faɗa wa kotun, kusan ɗalibai 30 sun fara sallah a harabar makaranta inda suke amfani da rigar su a matsayin darduma.
Makarantar ta bijiro da haramcin ne saboda damuwar da aka nuna wajen nuna wariya tsakanin mabiya addinai.