Home Labarai Haramcin Shiga Kasa: Najeriya Ta Gargadi Birtaniya

Haramcin Shiga Kasa: Najeriya Ta Gargadi Birtaniya

93
0
Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga gwamnatin Birtaniya ta janye matakin hana shiga ƙasar daga Najeriya sakamakon bullar sabon nau’in korona na Omicron.

Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga gwamnatin Birtaniya ta janye matakin hana shiga ƙasar daga Najeriya sakamakon bullar sabon nau’in korona na Omicron.

Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu Lai Mohammed, ya yi kiran yayin wani taron manema labarai a Abuja, yana mai cewa babu hikima a matakin.

Ya ce duk da cewa kwamatin yaƙi da korona na shugaban ƙasa zai ɗauki matakin da ya dace, amma a matsayin sa na mai magana da yawun gwamnati yana kallon matakin a matsayin zalinci da horo.

Lai Muhammad ya ƙara da cewa matakin na Birtaniya ba a ɗauke shi ta fuskar kimiyya ba, sannan ya bayyana mamakin sa kan yadda za a ɗauki matakin kan ƙasa mai al’umma fiye da miliyan 200, kawai saboda tsirarun mutanen da suka kamu da cutar.

A halin da ake ciki dai ofishin jakadancin Birtaniya a Najewriya ya dakatar da bayar da biza ga ‘yan Najeriyar sakamakon haramcin tafiyar da aka sa, shi ma kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na British Airways ya soke dukkanin tikitin shiga Birtaniya daga Najeriya, inda ya nemi fasinjojin su sauya lokaci ko kuma wurin tafiya.

Dikar Shiga Birtaniya: Adesina Ya Ce Wariya Ce Da Rashin Hikima

Shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka Akinwumi Adesina ya siffanta hana wasu ‘yan ƙasashen Afirka shiga wasu ƙasashen Turai saboda cutar korona a matsayin wariya da ke barazana ga rayuwar mutane.

Mista Adesina wanda tsohon ministan noma ne a Najeriya, ya bayyana hakan ne a shafin sa na Twitter, yana mai cewa ba daga Afirka annobar ta fito ba.

Ya ce tun da yanzu an samu Omicron a ƙasashen duniya da yawa kuma manya, me ya sa ba a hana ‘yan ƙasashen shiga ƙasashe ba sai Afirka kaɗai aka ware wanda rashin adalci ne matuƙa da wariya wanda kuma babu hikima a ciki.

Yanzu haka ofishin jakadancin Birtaniya a Najewriya ya dakatar da bayar da biza ga ‘yan Najeriyar sakamakon haramcin tafiyar da aka saka.

A yau Litinin ne haramcin shiga Birtaniya kan ‘yan Najeriya da wasu ƙasashen Afirka 10 ya fara aiki saboda abin da gwamnatin ƙasar ta kira na yaƙi da nau’in cutar korona na Omicron da ya ɓulla a ƙasashe da dama.