Majalisar wakilai ta bukaci Babban Bankin Nijeriya ya dakatar da umarnin da ya ba bankuna cewa su karbi kashi biyu zuwa biyar cikin 100 na kudaden da jama’a su ka shigar ko su ka fitar daga asusun ajiyar su.
Karanta Wannan: Sarrafa Kudade: CBN Ya Yi Hadaka Da Masallatai Da Coci-Coci
Matakin dai, ya bukaci cire kason a duk kudaden da aka fitar ko shigar matukar sun kai naira dubu 500 ga daidaikun mutane da kuma naira miliyan uku ga kamfanoni.
Yayin zaman ta na ranar Alhamis da ta gabata, Majalisar ta kafa kwamitin da zai yi nazari a kan hanya mafi dacewa ta aiwatar da wannan manufa.
Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa ya shaida wa manema labarai cewa, matakin da Babban Bankin ya dauka, masu kanana da matsakaitan masana’antu ne zai fi shafa.
Ya ce tun lokacin mulkin tsohon shugaban babban bankin Nijeriya Mai martaba sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi ne aka fito da tsarin, amma tsarin na yanzu ya sha bamban da na baya.