Home Home Har Da Hijabi Gwamnatin Zamfara Ta Sata A Gidana – Bello Mawalle

Har Da Hijabi Gwamnatin Zamfara Ta Sata A Gidana – Bello Mawalle

93
0

Tsohon gwamnan Jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle, ya ce sata aka je yi gidan sa bayan gwamnatin jihar ta ce ta ƙwato wasu motoci daga gidan sa, wadanda ya ƙi maidawa gidan gwamnati.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, gwamnatin jihar Zamfara ta ce jami’an tsaro sun shiga gidajen Matawallae biyu da ke Gusau da Maradun, inda su ka ƙwato motoci har guda 40.

Sai dai Matawalle ya ce tsagwaron talauci ne ya sa aka shiga gidajen sa, ya na mai cewa an sace kayayyaki ciki har da hijabin matan sa.

Ya ce duk ɗakunan matan shi babu wanda ba a shiga ba, inda hatta irin murhun nan na garwashi duk an sa a cikin mota an tafi da su.

Matawalle ya kara da cewa, wasu daga cikin motocin da aka kwashe ya sayo su ne daga Amurka tun kafin ya zama gwamna, saboda da ma can sana’arsa ce saida motoci.

Leave a Reply