Jamhuriyar Nijar ta fara ƙoƙarin sake rubuta tarihinta, wanda a yanzu ya fi ta’aƙalla da mulkin mallaka.
Matakin na zuwa ne bayan shugaban mulkin soja, Janar Abdourahamane Tiani ya kafa wani kwamitin wucin gadi da aka ɗora wa alhakin wannan gagarumin aiki.
Tun bayan juyin mulkin da Tiani ya yi Mohamad Bazoum, sabon shugaban na mulkin soji yake ta ɗaukar wasu matakai na rabuwa da abubuwa da suke alaƙanta ƙasar da Nijar.
A watannin baya ne aka sauya sunan wasu manyan titunan ƙasar, inda suka cire sunayen Farasanci.