Home Home Hannatu Musawa Ta Ƙaryata Rahoton Cewa Ta Ce  Babu Laifi Ta Na...

Hannatu Musawa Ta Ƙaryata Rahoton Cewa Ta Ce  Babu Laifi Ta Na Minista Kuma Ta Na NYSC

2
0

Ministar Al’adu Hannatu Musawa, ta ƙaryata rahoton da ke cewa ta ce ba ta karya doka ba don ta na minista kuma ta na aikin yi wa kasa hidima NYSC.

A wata sanarwa da mataimakin Daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar Al’adu Suleiman Haruna ya fitar, ya ce ministar ba ta fidda wata takarda da ake kafa hujja da ita a kafafen yaɗa labarai cewa daga wurin ta ne.

Ya ce Hannatu Musawa ba ta fidda wata takarda da ke cewa ta ce  ba ta ga laifin da ta aikata ba don ta na minista kuma ta na aikin yi wa kasa hidima ba.

Suleiman Haruna, ya ce babu gaskiya a cikin labarun, don haka ya ce ministar ta bukaci ‘yan jarida su riƙa tantance abubuwan da su ke yadawa don gudun saba ka’ida.