Home Labaru Hana Damfara: Rundunar Sojin Sama Ta Najeriya Ta Ce Kyauta Ta Ke...

Hana Damfara: Rundunar Sojin Sama Ta Najeriya Ta Ce Kyauta Ta Ke Daukar Sabbin Ma’aikata

430
0

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce daukar sabbin jami’an soji da take yi kyauta ne, kuma a bayyane ake yi ba tare da an biya wani ko wata hukuma ba.
Mai Magana da yawun rundunar sojin Air Commodore Ibikunle Daramola, ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Daramola, ya ce rundunar sojin saman ta samu labarin cewa wasu mutane na karbar kudade daga hannun wasu masu neman aiki da sunan za su musu hanya.