Sabon shugaban kamfanin mai na Kasa NNPC Mele Kyari, ya fara yin tankade da rairaya a duk kamfanoni da hukumomin da ke karkashin kamfanin NNPC.
Wata majiya ta ce sashen kula da kasuwanci da hada-hadar danyen mai NPDC ne shirin zai fi shafa.
Mele Kyari, ya ce wannan garambawul ya zama dole, matukar ana son a cigaba tare da gyara ayyukan matatar man gaba daya.
Yayin wata zantawa da ya yi da manema labarai, Kyar ya ce wasu manyan daraktoci sun maida kamfanin NNPC tamkar shagunan su ko gidajen su, kuma babu yadda aka iya da su.
Ya ce Ire-iren wadannan harkalloli dole a dakatar da su, sannan a sanya sabbin hannu a wadannan wurare idan har ana so a cigaba, ya na mai cewa, ba zai bari wasu su rika yin abin da su ka dama da dukiyar kasa ba.
Tuni dai hukumar NPDC ta rubuta wa kamfanonin da ke aikin hako danyen mai wasikun gargadi cewa, su maida hankali wajen sama wa mutanen kauyukan da su ke aiki ababen more rayuwa yadda ya kamata, tare da biyan haraji da kuma maido duk kudaden da ya kamata a zuba a asusun gwamnati.