Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya soki yadda gwamnatin Najeriya ta ke biye wa kasashen duniya game da annobar Korona da ake fama da ita a duniya baki daya.
Gwaman Yahaya Bello, ya ce bai ga dalilin da zai sa gwamnatin Najeriya ta rika kashe makudan kudade da sunan wai ana yaki da yaduwar korona ba.
Ya ce Idan ana sanyi a kasashen Turai da Amurka suna sa kayan sanyi ne mu kuma a kasar mu Najeriya muna sa kaya wanda ba na sanyi ba, kuma ma fanka da AC muke sakawa saboda zafi dan haka Menene zai sa dole sai yadda turawa suke so muma a wannan yankin za mu yi.
Ya hakikan ce cewa ba su da cutar Korona a jihar Kogi saboda haka ba za su kirkiro ta da karfin tsiya ba.
Yahaya Bello, ya ce sun yi wa mutane da dama gwaji a jihar babu wanda aka samu ya kamu da cutar , a sani basu da Korona wani ba zai zo ya hakikance ewa sai dole sun ce suna da masu cutar ba.
You must log in to post a comment.