Home Labaru Hajjin Bana: Za A Fara Jigilar Dawo Da Alhazan Nijriya Ranar 17...

Hajjin Bana: Za A Fara Jigilar Dawo Da Alhazan Nijriya Ranar 17 Ga Watan Agusta

883
0

Rahotanni na cewa, za a fara jigilar maido alhazan Nijeriya daga ranar Asabar, 17 ga watan Agusta na shekara ta 2019 bayan kammala aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya.

Shugaban kula da harkokin jirgin sama na hukumar alhazai ta Nijeriya Injiniya Mohammed Goni ya bayyana haka, yayin wani taro da masu ruwa da tsaki da ya gudana a Makkah ranar Alhamis da ta gabata.

Injiniya Goni, yace jirgin farko daga kamfanin Flynas, da ke dauke da alhazan jihar Lagos zai tashi da misalin karfe 7:00 na ranar 1 ga watan Agusta, yayin da jirgi na biyar zai kwashi alhazan jihar Kebbi.

Mohammed Goni, ya bukaci jami’ai daga hukumar aikin hajji na jihohi su hada kai da hukumar, sannan su tabbatar mahajattan ba su dauki jakunkuna da yawa ba.

Ana sa ran cewa, jirage biyu da za su kwashi mahajjata za su kasance a filin jirgin sama na sarki Abdlaziz da ke Jeddah, a ranar 16 ga watan Agusta domin fara jigilar mahajjatan Nijeriya.

Leave a Reply