Home Labaru Hajjin Bana: Hukumar Aikin Hajji Ta Kaduna Ta Sa Ranar Rufe Karbar...

Hajjin Bana: Hukumar Aikin Hajji Ta Kaduna Ta Sa Ranar Rufe Karbar Kudi

463
0

Hukumar aikin Hajji ta jihar Kaduna ta ayyana ranar 20 ga watan Yunin 2019, a matsayin ranar da hukumar za ta rufe karbar biyan kudin aikin hajjin bana.
Kakakin Hukumar, Yunusa Abdullahi, ne ya bayyana hakan ga menama labarai a Kaduna.
Yunusa, ya ce wannan matakin ya zama dole ne domin ganin an cimma matsaya da hukumar aikin hajjin ta kasa wato NAHCON ta ayyana akan muhimmancin kammala dukkanin wani shirye-shirye zuwa ranar 21 ga watan Yunin 2019.
Yunusa ya tabbatar da cewa wadanda suka saba wa wannan ka’idar akwai yiwuwar ba za su je aikin hajjin ba a bana.
Rahotanni sun bayyana cewa an ba jihar Kaduna kujera 6,636 a wannan shekarar, amma zuwa yanzu mutum 3,000 ne kawai suka yi rijistan aikin hajjin a bana.