Home Labaru Gyaran Fuska: Majalisa Ta Sauya Dokar Hukumar Kula Da Zuba Jari Ta...

Gyaran Fuska: Majalisa Ta Sauya Dokar Hukumar Kula Da Zuba Jari Ta Kasa

47
0

Majalisar Dattawa ta yi wa dokar hukumar kula da Zuba Jari ta Najeriya wacce aka fi sani da NSIP kwaskwarima da nufin dauke hukumar daga ma’aikatar agaji da rage talauci zuwa fadar shugaban kasa.

Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa Opeyemi Bamidele, ne ya kawo kudurin gyaran dokar, inda ya bayyana cewa manufar tsarin na da kyau, sai dai ba a ba da dama tsarin ya cimma manufofin kafa shi ba.

Opeyemi ya ce a majalisa ta 9 aka amince da kudurin amma an gano cewa aiwatar da shi na da kura-kurai, domin wadanda ya kamata a basu goyon baya wajen cin moriyar tsarin a yankunan karkara ba su ne suka amfana ba.

Sanata Mohammed Ali Ndume na daga cikin wadanda suka goyi bayan kudurin, inda ya ce wadanda aka ba su damar aiwatar da tsarin sun yi babakere a kai, ba su ba da dama majalisa ta sa ido a kan yadda aka gudanar da tsarin ba.

Ali Ndume ya ce Majalisa ta amince da dokar da za ta mayar da tsarin zuwa fadar Shugaban kasa ba tare da bata lokaci ba, ya kara da cewa a yanzu haka gwamnati tana bincike kan tsarin saboda kar a sake maimaita abin da ya faru a baya.