Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Gwamnonin Jihohi Sun Goyi Bayan Cire Tallafin Man Fetur A Najeriya

Gwamnonin jihohin Nijeriya, sun nuna goyon bayan su ga
matakin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na cire
tallafin man fetur.

Rahotanni sun ce, Gwamnonin sun bayyana haka ne yayin wata ganawa da su ka yi da shugaba Tinubu a fadar sa da ke Abuja.

Wata sanarwa da da daraktan yaɗa labarai na fadar shugaban kasa Abiodun Oladunjoye ya fitar, ta ce gwamnonin sun riƙa yin jawabi ɗaya bayan ɗaya a lokacin ganawar, inda su ka yaba wa shugaba Tinubu a kan matakin da ya ɗauka.

Gwamnonin, waɗanda su ka je fadar bisa jagorancin shugaban ƙungiyar gwamnonin Nijeriya kuma gwamnan jihar Kwara Abdul-Rahman Abdul-Razaq, sun ce za su yi aiki tare da shugaba Tinubu wajen ganin an magance matsalolin da cire tallafin zai haifar.

Exit mobile version