Kungiyar lauyoyi ta kasa NBA reshen jihar Ondo ta yi kira ga gwamnonin jihohi su yi amfani da kudaden tsaro da ake ba su domin biyan kudaden fansa daga hannun masu garkuwa da mutane.
Karanta Garkuwa Da Mutane: Gwamna Masari Ya Nemi A Daina Biyan Kudin Fansa
Karanta Wannan: Samar Da Kudaden Shiga: Gwamnonin Nijeriya Sun Gudanar Da Babban Taro A Abuja
Shugaban kungiyar Tajuddeen Ahmad ya bayyana haka a lokacin bikin mako da kungiyar ta shirya a a jihar Ondo, sannan ya ce idan gwamnoni suka yadda da wannan tsari, to gwamnonin za su cika aikin su na samar da tsaro ga al’ummomin su.
Ahmad ya kara da cewa, amfanin wadannan kudade shine, samar da tsaro ga mutane, saboda haka idan aka yi garkuwa da mutane to kamata ya yi ayi anfani da kudaden wajen ceto su daga hannu wadanda su ka yi garkuwa da su.
Ya kuma kara da cewa, idan an yi garkuwa da karamin ma’aikaci ko talaka, ina ake tunanin zai samo wadannan kudaden domin ya biya kudin fansa sa, saboda haka idan gwamnoni su ka yi anfani da kudaden tsaro da ake ba su tabbas za a san cewa suna aikin su.
Ahmad ya kuma yi Allah wadai da irin yawan sace sacen mutane da ke ayi a fadin kasar nan, inda ya ce an shiga wannan matsanancin halin ne sakamakon cin hanci da rashawada ake fama da shi a Nijeriya.
You must log in to post a comment.