Home Labaru Gwamnoni Su Na Fakewa Da Buhari Wajen Ɓoye Rashin Ƙwazon Su –...

Gwamnoni Su Na Fakewa Da Buhari Wajen Ɓoye Rashin Ƙwazon Su – Femi Adesina

107
0

Mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar yada labarai Femi Adesina, ya zargi wasu gwamnoni da fakewa da shugaba Buhari sun a boye rashin kwazon su.

A  wani sako da ya wallafa a shafin sa na Facebook, Adesina ya ce gwamnonin su kan dora laifi a kan shugaba Buhari ko da kuwa su na da hannu a ciki.

Ya ce shugaban kasa bay a da matsala da kowa, ciki kuwa har da masu sukar lamirin sa a cikin gwamnonin, amma duk da haka sun zabi su rika dora laifi a kan sa.

Femi Adesina, ya ce akwai gwamnonin da ke zagin shugaba Buhari kuma su nufi fadar sa domin neman mafaka, amma duk da haka kofar shi a bude ta ke gare su.

Ya ce wasu gwamnoni su na tunanin wata nasara ko jarumta su ke yi idan sun soki shugaban kasa, musamman idan sun rike albashi da fanshon jama’a sai su dora laifin a kan sa duk don su kauda hankalin al’ummar su daga lamarin fansho da albashi.