Home Home Gwamnatin Zamfara Za Ta Yi Haɗin Gwiwa Da Sweden Kan Haƙar Ma’adanai...

Gwamnatin Zamfara Za Ta Yi Haɗin Gwiwa Da Sweden Kan Haƙar Ma’adanai Da Noma

30
0

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana shirinta na hada gwiwa da kasar Sweden domin habaka harkokin hakar ma’adanai da Noma da Makamashi da Ilimi da kuma Kiwon lafiya.

Mai taimaka wa gwamnan jihar Dauda Lawal a kan harkokin yada labarai Sulaiman Bala Idris ya bayyana haka a wata sanarwa ya raba wa manema labarai.

Sanarwar ta ce gwamna Lawal ya tabbatar da haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin jakadiyar kasar Sweden a Nijeriya Annika Hahn-Englund a ofishinsa da ke Abuja.

Idris ya kara da cewa, gwamna Lawal ya kuduri aniyar binciko hanyoyin da za a bi domin jawo masu sa jari daga kasashen waje da tallafi daga abokan hulda na kasa da kasa da kuma na cikin gida.

Gwamna Lawal ya tabbatar wa Jakadar Sweden cewa, a shirye gwamnatinsa ta ke na ganin ta inganta hadin gwiwa domin samar ci gaba mai dorewa a bangarori daban-daban. Anata jawabin, jakadar ta yi alkawarin ba jihar Zamfara goyon baya a fannin hako ma’adanai da dabarun noma na zamani, samar da makamashi da inganta harkokin ilimi da kiwon lafiya.

Leave a Reply