Home Labaru Gwamnatin Za Ta Sake Duba Yadda Ake Tsarin Rabo Kudaden Shiga

Gwamnatin Za Ta Sake Duba Yadda Ake Tsarin Rabo Kudaden Shiga

377
0
Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta GWAMNATIN ce za ta kafa wani kwamiti  nan da mako mai zuwa wanda zai sake yin dubi kan yanda ake rarraba kudaden shiga na kasa a tsakanin gwamnatin tarayya, da Jihohi da kuma kananan hukumomi, ta la’akari da halin matsin tattalin arziki da ake fama da shi.

Shugaban hukumar tattara kudaden shiga na Najeriya RMAFC, Elias Mbam, ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, jim kadan da karbar lambar yabo na Civil Service Union.

Karanta Wannan: Juyin-Juya-Hali: Sowore Ya Ce Ba Gudu Ba Ja Da Baya

Wani bincike na cewa yanda ake rabon kudaden shiga a halin yanzun, gwamnatin tarayya tana samun kashi 52.68 ne, gwamnatocin Jihohi suna samun kashi 26.72 sai kananan hukumomi da suke samun kashi 20.60 na dukkanin kudaden da suka shiga asusun gwamnatin tarayya.

Hakanan kashi 13 na dukkanin kudaden mai da iskar gas da gwamnatin ta tarayya ta karba ana mayar da shi ne ga Jihohin da ake tatso man daga cikin su, domin a saka masu a kan matsalolin zaizayar kasa da suke fama da su a sabili da man da ake tonowa.

An shirya wannan tsarin ne a zamanin gwamnatin tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo, sai dai, hukumar rabon tattalin arzikin ta RMAFC, ta ga da bukatar a sake yin dubi a kan yanda ake yin rabon tun a shekarar 2013, domin a samu daidaiton samar da ci gaba a cikin kasa, inda ta shiga tattaunawa tare da ganawa da wasu fitattu a kan al’amarin.

Leave a Reply