Home Home Gwamnatin Tinubu Ta Fito Da Tsare-Tsaren Bunƙasa Tattalin Arziki Da Samar Da...

Gwamnatin Tinubu Ta Fito Da Tsare-Tsaren Bunƙasa Tattalin Arziki Da Samar Da Aiki

148
0

Gwamnatin tarayya ta fito da wasu tsare-tsare da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki tare da samar da aikin yi ga ‘yan Nijeriya.

Ministar masana’antu da kasuwanci da zuba Jari Dakta Doris Uzoka-Anite ta bayyana haka a wani taro na musamman da ma’aikatar yaɗa labarai ta shirya a Abuja.

A lokacin taron wanda ministan yada labarai Muhammad Idris Malagi ya jogoranta, an bayyana wa manema labarai irin ci gaban da aka samar a watanni shida, da kuma irin alƙiblar da za a fuskanta a nan gaba.

Idris Malagi ya tabbatarwa mahalarta taron cewa,  sun taru ne  domin gina ginshiƙin yarda da amana a tsakaninsu da ‘yan jarida, domin ganin ana sanarwa ‘yan Nijeriya abunda ake aiwatar wa.

Ya ce taron y aba ‘yan jarida damar gana kai-tsaye da manyan jami’an gwamnati, domin su yi tambayoyin da suka cancanta, musamman waɗanda suka shige wa ‘yan Nijeriya duhu.

Malagi ya kuma jaddada ƙoƙarin da ma’aikatarsa ke yi wajen yin komai a fili ba tare da ƙumbiya-ƙumbiya ba, sannan ya ce suna ƙoƙarin ganin ana yaɗa labarai a kusa da nesa, musamman ta hanyar da aka saba da kuma sabbin hanyoyin na’urorin zamani masu kai saƙonni nan take.

Leave a Reply