Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Gwamnatin Tarayya Ta Kara Kudin Wutar Lantarki A Boye – Bincike

Electricity

Wani bincike ya nuna cewa, gwamnatin tarayya ta kara kudin wutar lantarkin ba tare da sanin ‘yan Nijeriya ba.

Binciken, wanda Jaridar Leadership ta gudanar ne ya bankado karin da aka yi a watan Satumba, kuma hakan na tabbatar da shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ke yi na janye tallafin lantarki.

Majiyoyi daga kamfanonin lantarki sun bayyana wa Jaridar cewa, an ki shaida wa jama’a ne don gudun abin da ka iya biyowa baya na korafe-korafe.

Jaridar ta kara da cewa, an aike wa Kakakin hukumar kula da lantarki ta Nijeriya Usman Arabi don ya tabbatar ko karyata lamarin amma bai amsa ba.  

Wata majiya ta ce, karin da aka yi na kashi 2 cikin 100 ne kawai, kuma hakan ya zama wajibi saboda gwamnati ba za ta iya ci-gaba da biyan kudin tallafi ba.

Exit mobile version