Home Labaru Gwamnatin Tarayya Ta Fito Da Sabon Lasisin Daura Aure

Gwamnatin Tarayya Ta Fito Da Sabon Lasisin Daura Aure

510
0

Gwamnatin Tarayya ta bullo da sabon Lasisin Daura Aure, wanda ya kunshi dukkan nau’ukan aurarrakin da ake daurawa a Nijeriya.

Georgina Ehuriah, Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida
Georgina Ehuriah, Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida

Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida Georgina Ehuriah ta sanar da haka, yayin da ta ke jawabi a wajen taron matakai da ka’idojin daura aure a Nijeriya da ya gudana a Abuja.

Ta ce ma’auratan da ba su mallaki katin shaidar daura auren su ba za su iya bude shafin yanar gizo na Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida domin su sabunta lasisin su.

Ehuriah ta kara da cewa, ba dukkan wuraren ibadu ba ne aka amince su daina daura aure ba, don haka ta shawarci ‘yan Nijeriya su tabbatar sun daura aure a wuraren da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta amince su rika daura aure.

A karshe ta yi korafin cewa, ‘yan Nijeriya ba su damu su rika yin rajistar daurin auren su ba bayan sun yi auren addini ko na gargajiya.