Home Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Fitar Da Jerin Sunayen Wasu Daraktoci 14 Don Zabar...

Gwamnatin Tarayya Ta Fitar Da Jerin Sunayen Wasu Daraktoci 14 Don Zabar Akanta Janar a Cikinsu

319
0

An fara shirye-shiryen nada sabon Babban Akantan Nijeriya, yayin da gwamnatin tarayya ta fitar da sunayen wasu daraktoci 14 da ke mataki na 17 a aikin gwamnati, saboda babu kowa a kan kujerar tun bayan dakatar da Ahmed Idris da aka yi bisa zargin karkatar da kudi har naira biliyan 80.

Wannan, ya na kunshe ne a cikin wata takarda dauke da sa hannun, daraktar gudanarwa ta ofishin Akanta Janar na tarayya Mariya Rufai, waddda shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya Dr Folasade Yemi-Esan ta karba.

Sunayen wadanda aka fitar kuwa sun hada da Muhammad Murtala Saleh, da Chizea Onochie Peter da Lydia Jafiya Shehu da Bakre Modupe Julianah da Ibrahim Sa’adiya Jibo, da Omachi Raymond Omenka da Danladi Comfort Zakiwi da kuma Abah George Fidelis.

Sauran sun hada da Mohammed Aminu ‘Yar Abba da Samuel Waziri da Mahmud Adam Kambari da Mohammed Magaji Doho da Mufutahu Bukolah da kuma Yusuf Abdullahi Musa na ma’aikatar yada labarai da al’adu.

Leave a Reply