Gwamnatin tarayya ta bada umurnin a ba dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC Abdulrasheed Bawa damar ganin lauyoyi da ‘yan’uwan sa.
Rahotanni sun ruwaito cewa, lauyoyi da ‘yan’uwan Abdulrasheed Bawa su na iya ganin sa na tsawon makonni yanzu.
Bayanai sun ce, kalubalen da ake fuskan ta shi ne, Abdulrasheed Bawa ya ki ba masu bincike hadin kai ta hanyar amsa masu tambayoyi da jawabai kamar yadda ake bukata.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunan ta, ta ce Abdulrasheed Bawa ya ki ba masu bincike hadin kai ta hanyar kin amsa tambayoyi.
Wani babban lauya ya ce an hana tawagar lauyoyin Abdulrasheed Bawa nema masa ‘yanci a kotu, saboda umurnin da mahaifin sa ya bada.
You must log in to post a comment.