Mai taikawa shugaban kasa, aka harkokin hulda da jama’a da kuma ‘yan jaridu Femi Adesina, ya tunatar da Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar cewa zaben shekara ta 2019 talakawa ne suka zabi shugaban da ya dace da su.
Femi Adesina, ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ake aikawa Atiku Abubakar, wanda ya biyo bayan zargin da jam’iyyar APC ta yi wa jam’iyyar PDP na cewa ta bayyana dan takarar ta a matsayin shugaban kasa na boye.
Jam’iyyar APC ta zargi dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar da kokarin sauya tsarin siyasar Najeriya da karfin tsiya, da kuma wasa da hankalin ‘yan Najeriya
Karanta Labaru Masu Alaka: Jam’iyyar APC Ta Yi Kira Ga Atiku Ya Kame Bakin Sa
Femi Adesina, ya fitar da wannan sanarwa ce bayan maganar da Atiku Abubakar ya yi akan gawarwakin sojojin Najeriya guda dubu daya da aka gano an binne su a boye, wanda ake tunanin mayakan Boko Haram ne suka kashe.
Gwamnatin tarayya ta shawarci Atiku cewar ya yi hakuri har lokacin da kotu za ta yanke hukunci akan karar da ya shigar na cewar an yi magudin zabe.