Home Labarai Gwamnatin Ta Taya Al’ummar Indiya Murnar Kammala Zaɓe

Gwamnatin Ta Taya Al’ummar Indiya Murnar Kammala Zaɓe

309
0
12180950 1716885281
12180950 1716885281

Gwamnatin tarayya ta taya al’ummar Indiya murnar kammala zaɓen ƙasar.

Cikin wata sanarwa da ministan harkokin ƙasashen waje na ƙasar, Yusuf Maitama Tugga ya wallafa a shafinsa na X,

ya bayyana Indiya da cikakkiyar mai bin tsarin dimokraɗiyya  a duniya.

Indayakara da cewa Wannan zaɓe na tarihi, da aka kwashe kwana 44 ana gudanarwa , shi ne babban zaɓe da aka taɓa yi a tarihi

mutum biliyan ɗaya da miliyan 400  ne suka kaɗa ƙuri’unsu a zaɓen da aka kwashe kusan wata guda ana gudanarwar.

A matsayinmu na masu ƙarfin dimokraɗiyya a Afirka, muna taya ku murnar kai wannan mataki a dimokradiyyance,

wanda hakan na cikin manyan ƙudurorinmu na ƙasashen waje”, in ji minsitan harkokin wajen na Najeriya.

Sai a ranar 4 ga watan Yuni ne za a sanar da sakamakon ƙarshe na zaɓen.

Masu sharhi dai na ganin jam’iyyar BJP ta Firaministan ƙasar Narendra Modi ce kan gaba a jerin waɗanda ke da damar lashe zaɓen.

Jam’iyya ko ƙawancen jam’iyyu na buƙatar lashe kujeru 272 a majalisar dokoki kafin kafa gwamnati a Indiya.

Leave a Reply